Najeriya-Korona

Najeriya za ta hana baki shigowa daga India, Brazil, Turkiya saboda Korona

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Twitter@BashirAhmaad

Hukumomin Najeriya sun sanar da shirin hana baki daga kasashen India da Brazil da kuma Turkiya zuwa kasar saboda barazanar yada cutar korona wadda ta yi kamari a cikin kasashen su.

Talla

Kwamitin shugaban kasa dake yaki da cutar ya sanar da cewar dokar ba ta shafi matafiyan da suka ratsa wadannan kasashe ba, sai dai mazauna kasashen wadanda ba 'yan Najeriya bane.

Kwamitin ya ce daukar wannan matakin kariya ya zama wajibi domin rage hadarin yada cutar wadda ake shiga da ita daga kasashen waje.

Sanarwar ta ce za’a killace 'yan Najeriya da kuma mazauna wadannan kasashe da suka kwashe kwanaki 14 a can kamar yadda ka’ida ta bayyana na mako guda a cibiyar da gwamnati ta ware duk lokacin da suka isa kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.