Tattalin Arziki - Najeriya

Asusun ajiyar ketare na Najeriya ya girgiza

Ginin Babban Bankin Najeriya CBN da aka dauka a watan nuwambar 2011.
Ginin Babban Bankin Najeriya CBN da aka dauka a watan nuwambar 2011. AP - Sunday Alamba

Najeriya ta yi asarar dala miliyan 350 asusun ajiyarta da ke waje cikin makonni biyu. A cewar sanarwar Babban Bankin Kasar CBN, ya zuwa ranar 29 ga watan Afrilu asusun ajiyar da ke waje ya ragu zuwa dala biliyan 34 da miliyan 900, sabanin yadda yake dala biliyan 35 da miliyan 250 daga 16 ga watan na Afrilu.

Talla

Alkaluman Babban Bankin Najeriya daga ranar litinin sun nuna cewa ajiyar, wacce ta fara farfadowa ta tashi zuwa daga dala biliyan 34 da miliyan 850 daga ranar 1 ga watan Afrilu ta soma rikotowa kasa a tsakiyar watan.

Tasirin Covid-19 kan kan kudaden ajiyar kasashen ketare

A lokacin CBN ya danganta habakar asusun ajiyar na waje da hauhawar farashin danyen mai a kwanan nan dangane da nasarar alluran rigakafin cutar COVID-19 da aka samu a fadin duniya.

Shi dai asusun ajiyar ketare, na matsayin ma’auni da ake ake amfani da shi wajen gane karfin tattalin arzikin kasa, tare da bai wa takardar kudin kasa daraja da cikakkiyar kariya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.