Najeriya-Boko Haram

Mayakan Boko Haram sun fantsama sassan jihar Bauchi- Gwamnati

Hare haren mayakan kungiyar a baya- bayan nan na ci gaba da tsananta a jihohin Yobe da Borno.
Hare haren mayakan kungiyar a baya- bayan nan na ci gaba da tsananta a jihohin Yobe da Borno. REUTERS - HANDOUT

Gwamnatin Jihar Bauchi da ke Najeriya ta yi shelar cewar yanzu haka mayakan boko haram sun kutsa kai cikin kananan hukumomin ta guda 4 da ke makotaka da Jihar Yobe.

Talla

Sakataren Gwamnatin Jihar Alh Sabiu Baba ya bayyana cewar kananan hukumomin sun hada da Zaki da Gamawa da Darazo da kuma Damban, yayin da ya ce  mayakan sun lalata turakun sadarwa a karamar hukumar Gamawa.

Baba ya ce gwamnatin Jihar ta gano wasu barazanar tsaron ake gani tattare da kwararar mutanen daga Jihar Yobe inda mayakan boko haram suka yi ta kai hare hare.

Sakataren ya ce gwamnatin Jihar ta gabatar da taimako ga jami’an tsaron jihar domin kara sa ido akan iyakar jihar da Yobe.

Kwamishinan 'yan Sandan Jihar Sylvester Abiodun Alabi ya ce za su hada kai da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a Jihar.

Kwamishinan ya nemi taimakon mazauna jihar wajen gabatar da bayanai ga hukumomin tsaro da kuma kaucewa boye wadanda ake zargin cewar bata gari ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.