Najeriya-Buhari

Rundunonin Sojin Najeriya sun yi watsi da shawarar yiwa Buhari juyin mulki

Shugabannin hafsoshin tsaron Najeriya a fadar gawamnatin kasar dake Abuja  yayin ganawar gaggawa kan tsaro ranar 30 ga watan Afrilun 2021 da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Shugabannin hafsoshin tsaron Najeriya a fadar gawamnatin kasar dake Abuja yayin ganawar gaggawa kan tsaro ranar 30 ga watan Afrilun 2021 da shugaban kasa Muhammadu Buhari. © Presidency of Nigeria

Rundunonin Sojin Najeriya sun yi watsi da shawarar kifar da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari sakamakon dimbin matsalolin tsaron da suka addabi kasar.

Talla

Sanarwar da ma’aikatan tsaron kasar ta gabatar mai dauke da sanya hannun Daraktan yada labaran ta Janar Onyema Nwachukwu ta ce sojojin za su cigaba da marawa gwamnatin baya wajen aikin samar da tsaro da kare dimokiradiya da kuma kaucewa shiga harkokin siyasa.

Daraktan ya ce yana da kyau mutane su fahimci cewar rundunonin sojin na mutunta gwamnatin da ke karagar mulki da kuma sauran bangarorin ta, kuma za su cigaba da goyawa shugaban kasa da ma babban kwamandan hafsan sojojin kasar baya kamar yadda kundin tsarin mulkin shekarar 1999 ya tanada.

Wannan dai ba shi ne karon farko da sojojin ke watsi da irin wadannan kiraye kiraye na kawar da gwamnatin kasar ba, yayinda su ke jaddada goyan bayan su ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A makon jiya 'yan Majalisun kasar sun bukaci shugaban kasa Buhari da ya kafa dokar ta baci kan bangaren tsaro domin kawo karshen kashe kashen da suka mamaye kasar sakamakon hare haren 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane da kuma mayakan boko haram.

Sanarwar sojin ta yi nuni da kalaman Robert Clarke wani fitaccen lauya da ya bukaci kawar da gwamnonin kasar da kafa dokar ta baci wajen nada sojojin da za su samar da tsaro a jihohin da ake fama da tashin hankali.

Clarke ya bayyana cewar Najeriya ta kama hanyar rugujewa, inda ya bukaci shugabannin siyasa da su bai wa sojoji dama domin dawo da tsaro a cikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.