'Yan bindiga sun kashe mutane 35 ciki har da sojoji a Najeriya

Makamin roka makale jikin wata mota da mayakan Boko Haram ke amfani da shi a garin Damasak dake jihar Barno, an dauki hoton ranar 18 ga watan Maris shekarar 2015
Makamin roka makale jikin wata mota da mayakan Boko Haram ke amfani da shi a garin Damasak dake jihar Barno, an dauki hoton ranar 18 ga watan Maris shekarar 2015 ASSOCIATED PRESS - Jerome Delay

A Najeriya, bayanai sun ce mayakan Boko Haram da ke alaka da IS sun kashE mutane 35 cikin su har da sojoji 5 da ‘Yan Sa-kai 15 a hare-hare guda 2 da suka kai arewacin Borno.

Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce mayakan a cikin motoci da dama da ke dauke da muggan makamai sun kai hari akan sansanin soji da ke garin Ajiri jiya litinin, abinda ya yi sanadiyar kashe 5 daga cikin sojojin tare da ‘-Yan Sakai 15.

Rahotanni sun ce mayakan sun fara kai hari ranar lahadi inda suka kashe kwamandan sojin tare da fararen hula guda 6 da kuma kwashe makamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.