Najeriya - Abia

'Yan bindiga sun sace daliban jami'ar jihar Abia

Hoton domin misali kan 'yan bindiga.
Hoton domin misali kan 'yan bindiga. © Depositphotos

Gwamnatin Abia ta tabbatar da rahoton sace wani adadi na daliban jami'ar jihar da gungun 'yan bindiga suka yi a daren ranar Larabar da ta gabata.

Talla

Yayin karin bayani kan lamarin cikin sanarwar da ya fitar, kwamishinan watsa labaran jihar ta Abia John Kalu, ya ce 'yan bindigar sun yiwa daliban kwanton Bauna ne a yayin da suke tafiya cikin motarsu akan hanyar Okigwe-Uturu.

Kwamishinan ya ce bayanan da suka soma samu sun nuna cewar an sace daliban dake kan hanyar zuwa Uturu daga Okigwe ne a tsakanin karfe 7 zuwa 8 na daren ranar Laraba.

Har yanzu dai ba a tantance yawan daliban da maharan suka yi awon gaba da su ba.

Awon gaba da daliban jami’ar jihar ta Abia shi ne satar daliban makarantar gaba da sakandire na baya bayan nan da ‘yan bindiga suka yi a Najeriya, bayan sace daliban jami’ar Greenfield da kuma na kwalejin horas da ayyukan gandun daji, dukkaninsu a jihar Kaduna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.