Najeriya-INEC

Kotun kolin Najeriya ta ba INEC izinin soke wasu jam'iyyun siyasa

Shugaban hukumar zabe na Najeriya INEC Farfesa Mahmud Yakubu.
Shugaban hukumar zabe na Najeriya INEC Farfesa Mahmud Yakubu. Ventures Africa

Kotun kolin Najeriya ta yanke hukuncin cewar hukumar zaben kasar na da hurumin soke wasu Jam’iyyun siyasar kasar da suka gaza wajen taka rawar lashe wasu kujerun majalisu ko na gwamnoni ko kuma shugaban kasa.

Talla

Wannan ya biyo bayan karar da Jam’iyyar NUP ta shigar inda ta ke kalubalantar hukumar zaben kan matakin da ta dauka na janye lasisin ta da na wasu jam’iyyun kasar 74.

Mai shari’a Chima Nweze ya ce matakin da hukumar zaben ta dauka ya yi daidai da dokar kasa da kuma dokar zabe da ake amfani da ita a kasar.

Kafin wannan hukunci na yau babban kotun Abuja da ta daukaka kara duk sun amince da matsayin hukumar zaben na soke lasisin Jam’iyyu 74 saboda gaza lashe koda kujerar majalisa guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI