Najeriya - Imo

Najeriya: Jami'an tsaro sun halaka 'yan bindigar IPOB da dama a Imo

Wani ofishin 'ya sanda a Najeriya.
Wani ofishin 'ya sanda a Najeriya. AFP

Hadin gwiwar jami’an tsaron Najeriya na sojoji da ‘yan sanda sun samu nasarar halaka ‘yan bindigar haramtacciyar kungiyar IPOB, yayin da suka kai hari kan babban ofishin ‘yan sanda na yankin Orlu dake jihar Imo.

Talla

Yayin fafatawar, jami’an tsaron Najeriyar sun kuma kwace motoci akalla 7 da ‘yan bindigar suka yi amfani da su wajen kaddamar da farmakin.

Rahotanni sun ce sai da aka shafe sa’o’i ana musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da maharan da ake kyautata zaton ‘ya’yan haramtacciyar kungiyar IPOB ne.

Cikin watan Afrilu ‘yan bindigar suka kai munanan hare-hare kan hukumomin tsaron Najeriya dake jihar Imo inda suka saki fursunoni kusan dubu 2.

Hare-haren ‘yan bindigar da ake zargin ‘yan kungiyar IPOB da kaiwa a wasu jihohin yankin kudu maso gabashin Najeriya sun karu a makwannin baya bayan nan,  inda ko a jihar Ebonyi, wasu ‘yan bindigar suka kai farmaki kan ofishin ‘yan sanda na Obiozara dake karamar hukumar Ohaozara a ranar Alhamis.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.