Najeriya - Anambra

'Yan bindiga sun kai hari kan ofishin 'yan sanda a Anambra

Wasu jami'an tsaron Najeriya a birnin Fatakwal.
Wasu jami'an tsaron Najeriya a birnin Fatakwal. AP - SCHALK VAN ZUYDAM

Gungun ‘yan bindigar da ake zaton ‘yan haramtacciyar kungiyar IPOB ne sun kai har ikan babban ofishin ‘yan sanda dake karamar hukumar Idemili ta arewa dake karamar hukumar Anambra, inda suka kashe jami’an ‘yan sanda 2, yayin musayar wutar da suka yi.

Talla

Rahotanni sun ce maharan sun kuma yi awon gaba da wani adadi na bindigogi kirar AK47, da tarin alburusai, tare da kone ofishin ‘yan sandan da suka dirarwa.

Har zuwa wannan lokaci dai babu hukumomin tsaron Najeriya basu kai ga tantance wadanda suka kai farmakin da misalin karfe 11 da rabi na daren ranar Alhamis ba.

Hare-haren ‘yan bindigar da ake zargin ‘yan kungiyar IPOB da kaiwa a wasu jihohin yankin kudu maso gabashin Najeriya sun karu a makwannin baya bayan nan,  inda ko a jihar Ebonyi, wasu ‘yan bindigar suka kai farmaki kan ofishin ‘yan sand ana Obiozara dake karamar hukumar Ohaozara.

Yayin farmakin maharan sun bankawa wasu sassan caji ofishin ‘yan sandan wuta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.