Najeriya-NLC

Kungiyar kwadago ta gargadi gwamnatin Najeriya kan rage albashin ma'aikata

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS - AFOLABI SOTUNDE

Kungiyar Kwadago a Najeriya ta gargadi gwamnatin kasar da kada ta kuskura ta ce za ta zaftare albashin ma’aikatanta sakamakon matsalar kudaden da ta ce tana fama da shi.

Talla

Kungiyar tace yin gaban gwamnatin na rage albashin ma’aikatan zai zama tamkar kisan kai ga ma’aikatan Najeriya wadanda ke dandanar kudar su dangane da tsadar rayuwa.

Shugaban kungiyar Ayuba Wabba yace bai dace ace gwamnati ta rage mafi karancina labashin da ake biya ba na naira 30,000 wanda a halin yanzu ko buhun shinkafa ba zai iya saye ba.

Waba yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ja kunnen ministan wajen ganin ta janye kalaman ta da kuma dakatar da duk wani yunkuri na rage albashin.

Wannan ya biyo bayan sanarwar da minister kudi Zainab Ahmed tayi cewar gwamnatin na nazarin rage tsadar kudaden da ake kashewa wajen tafiyar da ayyukan ta wanda ya hada da rage albashin ma’aikata.

Ministar tace tuni ta baiwa Hukumar dake kula da albashin ma’aikata umurnin sake Nazari kan albashin ma’aiaktan gwamnatin tarayya da kuma yawan hukumomin da ake da su domin bada shawara akai.

 

s

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.