Najeriya - Neja

Mutane kusan 30 sun mutu bayan kifewar kwalekwale a jihar Neja

Wani bangare na kogin Neja da Benue a Najeriya.
Wani bangare na kogin Neja da Benue a Najeriya. © Daily Trust

Masu linkaya sun tsamo gawarwakin mutane kimanin 30 da suka rasa rayukansu sakamakon kifewar da kwalekwalensu yayi cikin kogi a jihar Neja dake Najeriya.

Talla

Masu aikin ceto a garin Tijana dake karamar hukumar Munya, sun ce har yanzu suna cigaba da laluben wasu mutanen 7 da suka bace, yayin da kuma suka samu nasarar ceto wasu 65.

Wadanda suka shaida hatsarin sun ce jirgin ruwan ya kife ne da misalin karfe 6 na yammacin jiya Asabar dauke da kimanin mutane 100, a yayin da suke kan hanyar komawa gidajensu daga cin kasuwar Zumba dake karamar hukumar Shiroro, a daidai lokacin da mamakon ruwan sama ke sauka.

Bayanai sun ce dukkanin fasinjojin da hatsarin ya rutsa da su, sun fito ne daga garuruwa kimanin 7 dake karamar hukumar Munya, inda ‘yan bindiga suka matsa da kaiwa hare-hare.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa a jihar ta Neja Inga Ahmed, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yayi karin bayanin cewar mutane 28 ne suka mutu, an ceto 65 yayin da ake neman wasu 7.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI