Najeriya-Tsaro

Gwamnonin kudancin Najeriya na son Buhari ya gaggauta kiran taron kasa kan tsaro

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AP - Bayo Omoboriowo

Gwamnonin Jihohi 17 da suka fito daga kudancin Najeriya sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta kiran taron kasa da zai tattauna halin da kasa ke ciki da kuma yiwa jama’a jawabi domin su fahimci abinda ke tafiya dangane da matsalar tsaron da ta dabaibaye kasar.

Talla

Gwamnonin sun kuma amince a tsakanin su da haramta kiwo a daukacin jihohin dake kudancin kasar saboda abinda suka kira matsalolin tsaron da kiwon ke haifarwa.

Gwamnonin sun dauki wannan matsayi ne lokacin da suka gudanar da taron su a Asaba dake Jihar Delta domin tattauna batutuwan da suka shafi Jihohin su da kuma kasa baki daya.

Kafin dai wannan lokaci, daidaikun Jihohin sun yi dokar haramta kiwon wanda akasari Fulani makiyaya daga arewacin kasar keyi, saboda rikice rikicen da aka dinga samu a baya bayan nan wanda ke kaiga rasa rayuka musamman tsakanin manoma da makiyayan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI