G7-Boko Haram

Kasashen G7 za su tallafawa wadanda rikicin Boko Haram ya shafa a Najeriya

Wasu 'yan jihar Borno dake zaman gudun hijira a birnin Yola dake jihar Adamawa saboda rikicin Boko Haram.
Wasu 'yan jihar Borno dake zaman gudun hijira a birnin Yola dake jihar Adamawa saboda rikicin Boko Haram. AP - Sunday Alamba

Kuniyar Kasashen G7 da ke da karfin tattalin arziki sun yi alkawarin bayar da gudumawar Dala miliyan 389 don taimakawa mutanen da rikicin boko haram ya shafa a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Talla

Sanarwar da ofishin Jakadancin Birtaniya da ke Najeriya ya gabatar ya ce Birtaniya na jagorancin kasashen G7 wajen tsara yadda za a gudanar da aikin jinkai a yankin a cikin wannan shekara.

Birtaniyar ta bukaci samar da tsaro wajen baiwa jami’an aikin jinkai damar shiga yankunan dake arewa maso gabas domin taimakawa mutanen da rikicin ya ritsa da su da aka kiyasta yawan su ya kai akalla miliyan guda.

Babbar jami’ar diflomasiyar Birtaniya a Najeriya, Catriona Laing ta ce ya zama wajibi su dauki mataki akai domin kaucewa tabarbarewar al’amuran samar da abinci ga miliyoyin mutanen da wannan rikici ya shafa.

Rikicin book haram da ya kwashe sama da shekaru 10 ya yi sanadiyar kasha mutane sama da 30 da kuma raba miliyoyin mutane da matsugunin su a Najeriya da kuma kasashen dake makotaka da kasar.

Taron kungiyar G7 da akayi a makon jiya a birnin London ya amince da ware Fam biliyan 5 domin gudanar da aikin jinkai a fadin duniya, ciki harad ware Fam biliyan guda ga kasashen Yemen da Sudan ta Kudu da Najeriya cikin gaggawa domin ceto rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI