Najeriya-Maiduguri

Rahoton kan addu'o'in da musulmi suka gudanar don neman tsaro a Najeriya

Wasu jami'an tsaron Najeriya, yayin aikin bayar da tsaro a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Wasu jami'an tsaron Najeriya, yayin aikin bayar da tsaro a yankin arewa maso gabashin Najeriya. © Lekan Oyekanmi/AP

Daruruwan mata ne daga kungiyoyin daban daban a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya suka gudanar da wata zanga-zangar lumana da kuma addu’o’in neman Allah Madaukakin Sarki ya kawo karshen zubar da jini da kuma kame mutane da ake yi ana garkuwa da su a sassan kasar.Zanga-Zangar da addu’o’in an gudanar da su ne karkashin kungiyar mata ‘yan jaridu wato NAWOJ a takaice, wadda kuma ta samu halartar sauran kungiyoyin mata mabiya addinin addinin musulunci da na kirista. Daga Maiduguri, ga rahoton wakilinmu Bilyamin Yusuf.