Najeriya-Tsaro

Najeriya: 'Yan sanda sun gano boyayyar makabarta a Binuwai

Wasu 'yan sanda Najeriya.
Wasu 'yan sanda Najeriya. © file.jpg

Rundunar ‘yan sandar jihar Benuwaia Najeriya ta gano wasu kaburburan sirri a karamar hukumar Kastina-Ala da ke jihar, bayan makamancinsa da aka taba gani a shekarar 2019.

Talla

Gano manyan kaburburan ya biyo bayan cafke wasu mutane biyu da ake zargi da aikata laifuka wadanda  ke biyayya ga Azonto, mataimakin kwamandan gungun ‘yan fashin nan, Terwase Akwaza, da aka fi sani da ‘Gana’ wanda jami’an tsaro suka kashe shi a watan Satumbar bara.

Shugaban karamar hukumar Kastina-Ala, Alfred Atera, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa an kama ‘yan bindigar biyu a Illesa da ke jihar Osun sannan aka dawo da su Binuwai.

Atera ya ce ranar Litinin wadanda ake zargin suka jagoranci hukumomi da jami'an tsaro zuwa wurin da suka aikata ta'asar a Kastina-Ala, inda suka amsa kisan mutane tara, inda suka binne hudu cikin rijiyar da ta kafe, sai kuma wasu biyu a cikin kabari mara zurfi tare da matansu.

A shekarar 2019 ma, an gano makamancin wannan kabari a garin Zaki Biam da ke karamar hukumar Ukum na jihar ta Benuwai, kana bayan makonni biyu aka sake gano manyan kaburbura dauke da mutane da dama, da ake zargin matsafa ne suka kashe kuma suka binne a karamar hukumar Ushongo dake jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI