Kano-Sallah

Yadda bukukuwan Sallah suka gudana a Jihar Kano ta Najeriya

Wani yanki na birnin Jihar Kano a Najeriya.
Wani yanki na birnin Jihar Kano a Najeriya. © REUTERS/LUC GNAGO

A jihar Kano da ke Najeriya an gudanar da bukukuwan sallah ne ba tare da wata fargaba ba, duk da sanarwar da aka bayar ta kame wasu ‘yan boko haram da jamian tsaron kasar suka yi a baya bayan nan cikin jihar. Wani abu da kanawan ke matukar murna da shi a wannan sallah, ita ce sanarwar da aka bayar cewa za a yi hawan daushe a sallar ta bana, kamar dai yadda za ku ji karin bayani a wanna rahoto da Abubakar Isa Dandago ya aiko mana daga Kano.