Nigeria - Rashawa

ICPC na neman surikin Buhari ruwa a jallo saboda ɓatan $65m

Headikwatar hukumar ICPC mai yakar laifukan cin hanci da rashawa a Najeriya.
Headikwatar hukumar ICPC mai yakar laifukan cin hanci da rashawa a Najeriya. Photo Credit: icpc.gov.ng

Hukuma mai zaman kanta dake yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ICPC ta ayyana Gimba Kumo, daya daga cikin surikan shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wanda take nema ruwa a jallo bisa zargin yayi almundahana da kudaden da suka kai dala miliyan 65.

Talla

Mista Kumo, wanda ya auri ‘yar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2016, ya aikta aika-aikar ce da wasu mutane biyu Tarry Rufus da kuma Bola Ogunsola.

Cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin ICPC, Azuka Ogugua, ICPC ta bukaci jama'a da su gabatar mata da duk wasu bayanai da za su taimaka mata wajen gano inda mutanen suke, ko kuma ofishin ‘yan sanda dake kusa da su.

“Duk wanda yake da wani bayani kan inda mutanen suke dangane da kudaden samar da gidaje ga ma'aikata da suka handame, yana iya ba da rahoto ga hedikwatar ICPC da ke Abuja ko ofisoshinta na jihohi ko ma ofishin ‘yan sanda da ke kusa,”

Fadar Buhari bata ce komai ba

Mista Kumo, tsohon daraktan gudanarwa na bankin Federal Mortgage ne karkashin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Ya zuwa lokacin wallafa labarin nan Fadar shugaban kasa bata fitar da wata sanarwa ba dangane da wannan batu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.