Najeriya - Kaduna

Ma'aikata sun shiga yajin aiki a Kaduna

Wasu 'ya'yan kungiyar kwadago a Najeriya.
Wasu 'ya'yan kungiyar kwadago a Najeriya. ASSOCIATED PRESS - SUNDAY ALAMBA

Mai’aikatan kamfanin rarraba hasken lantarki da kuma na tashar jiragen kasa da na sama a Kaduna sun sha alwashin tsayar da muhimman lamurran hada-hadar yau da kulla a jihar, sakamakon yajin aikin da kungiyar kwadago tayi shelar shiga.

Talla

Gamayyar kungiyoyin kwadagon ma’aikatan sun bayyana matakin na su ne cikin wata sanrwar hadin gwiwa da suka sanyawa hannu.

Kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC reshen Kaduna za ta soma yajin aikin daga yau Lahadi ne domin adawa da wasu manufofin gwamnatin jihar, wadanda suka ce na haifar da mummunar Illa ga ma’aikata, musamman ma matakin baya bayan nan da gwamnati malam Nasir El Rufa’i ta dauka na sallamar ma’aikata da dama a fannoni daban daban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.