Najeriya-Tsaro

Najeriya: Igboho ya yi barazanar kawo cikas a zaben 2023

Sunday Adeyemo, mai ikirarin kare hakkin Yarabawa a Najeriya.
Sunday Adeyemo, mai ikirarin kare hakkin Yarabawa a Najeriya. © twitter

Mutumin nan mai ikirarin kare hakkin ‘yan kabilar Yarabawa a Najeriya, Sunday Adeyemo, ya yi barazanar kawo cikasa   babba zaben shekarar 2023 a kudu masu yammacin kasar

Talla

Mr Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya bayyana haka ne a birnin Osobgo, a yayin wani gangami na kabilar Yarabawan, inda masu halartasa suka nemi ballewa daga kasar.

Ya yi ikirarin cewa yawancin gwamnaonin kudu maso yammacin kasar na sha’awar ballewa amma kuma tsoron kada a hana su kudin jiha na wata-wata ya hana su furtawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.