Kaduna - Hakkin dan Adam

Kungiyar kwadago ta jagoranci zanga-zanga kan korar ma'aikata a Kaduna

Wasu 'ya'yan kungiyar kwadago yayin zanga-zangar adawa da korar ma'aikata a jihar Kaduna.
Wasu 'ya'yan kungiyar kwadago yayin zanga-zangar adawa da korar ma'aikata a jihar Kaduna. © Suleiman Shuaibu / BJO/HB/NAN

‘Yan’yan kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC sun gudanar da zanga-zanga a garin Kaduna, domin bayyana bacin rai da kuma nuna adawa kan matakin gwamnatin jihar na sallamar dubban ma’aikata daga bakin aiki, a matakan jiha da na kananan hukumomi.

Talla

Tun a ranar lahadin da ta gabata ne dai, gammayar kungiyoyin ma’aikatan fannoni daban daban a jihar ta Kaduna da suka hada da na filin jirgin kasa da na sama da kuma ma’aikatan kamfanin rarraba samar da hasken lantarki, suka sha alwashin tsaida ayyukansu domin biyayya ga uwar kungiyarsu ta kasa da ta bada umarnin shiga yajin aiki a daukacin jihar.

Yayin jawabi ga taron zanga-zangar, shugaban kungiyar kwadagon Najeriya na kasa Ayuba Wabba, ya ce gwamnati ba ta bi ka’idojin da doka ta shimfida ba wajen zartas da matakin sallamar dubban ma’aikatan da ta yi ba.

Yajin aiki ya janyo karancin man fetur da hasken lantarki

Rahotanni sun ce an samu layin ababen hawa a gidajen sayar da man fetur dake sassan Kaduna tun daga ranar Lahadi sakamakon matakin shiga yajin aikin na kungiyar NLC.

Zalika an samu katsewar samun hasken wutar lantar a sassan jihar ta Kaduna a sakamakon yajin aikin kungiyar kwadagon ta NLC da ma’aikatan fannin suka marawa baya.

Sai dai a na ta bangare, gwamnatin jihar Kaduna ta hannun shugabar ma’aikatanta Bara’atu Muhammad, ta ce yajin aikin gargadin na kwanaki 5 da ma’aikatan suka fara daga ranar Litinin, ba zai hana ta yin gyara ga tsarin aiki a jihar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI