Najeriya - 'Yan bindiga

'Yan bindiga sun harbe direba tare da sace fasinjoji 13 a Nasarawa

Hoton domin misali kan 'yan bindiga.
Hoton domin misali kan 'yan bindiga. © Depositphotos

'Yan bindigar dake garkuwa da mutane a Najeriya sun hallaka wani direbar motar safa akan hanyar Shafa-Abakpa zuwa Umaisha dake karamar hukumar Toto a Jihar Nasarawa inda suka kwashe fasinjoji 13 suka gudu da su.

Talla

Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriya tace direban motar ya rasu a asibitin koyarwar Jami’ar Abuja sakamakon harsasai 3 da 'Yan bindigar suka dirka masa a ciki lokacin kai harin.

Wani direba da ya tsallake da ya tsallake rijiya da baya lokacin harin, Ibrahim Saidu yace 'Yan bindigar sun tare motocin ne da misalign karfe 5 na yammacin jiya, bayan sun bullo daga daji zuwa bakin hanya dauke da makamai, inda suka tare motoci guda 4 da suka fito daga kauyen Ugya.

Direban yace motocin guda 4 da aka tare na dauke da fasinjojin da suka dauko daga kauyen ne zuwa Abaji da Toto.

Ana kai hari jifa-jifa

Basaraken Yankin, Ohimegye Panda, Usman Abdullahi yace sun dade suna fuskantar wannan matsala daga Yan bindigar dake zama a cikin dazukan yankin, wanda jifa-jifa suke kai hari kan matafiya.

Abdullahi ya bukaci gwamnatin jihar Nasarawa da ta hada kai da ta tarayya domin daukar matakin kakkabe Yan bindigar dake yankin.

Rahotanni sun ce makwanni biyu da suka gabata, 'Yan bindigar sun tare wasu 'Yan kasuwar kauyen Ugya inda suka yi awon gaba da 9 daga cikin su, harda sanda aka biya naira miliyan 9 kafin sakin su.

Kakakin rundunar Yan Sandan Jihar Nasarawa Nansel Rahman yace ya zuwa wannan lokaci basu samu labarin harin ba daga ofishin su dake karamar hukumar Toto.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI