Najeriya - Boko Haram

Shekau ya yi yunkurin hallaka kansa bayan da ISWAP ta far masa

Shugaban kungiyar mayakan Boko Haram Abubakar Shekau, an dauki hoton a watan Janairun 2018
Shugaban kungiyar mayakan Boko Haram Abubakar Shekau, an dauki hoton a watan Janairun 2018 BOKO HARAM/AFP/File

Rahotanni daga Najeriya na cewa, Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya samu mummunan rauni bayan da ya yi kokarin kashe kansa don kauce wa shiga hannu, yayin artabu da kishiyarta dake biyayya ga IS.

Talla

Wasu jami’an leken asiri biyu ne dai suka shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar, shugaban na Boko Haram Abubakar Shekau yayi yunkurin hallaka kansa ta hanyar harbin kansa a kirji lokacin da mayakan Iswap suka mamaye su a dajin Sambisa ranar Laraba, inda suka bukace shi da ya mika kai.

Kafin wasu daga cikin baradensa sukayi nasarar tserewa da shi tudun mun tsira bayan ya samu mummunar rauni.

Majiyar leken asiri ta biyu ta ce Shekau ya samu mummunan raunin ne bayan tayar da bama-baman da ke jikinsa a cikin gidan da yake boye da wasu mukarrabansa lokacin da mayakan na ISWAP suka far musu.

Bangarorin biyu basa ga maciji da juna

Bangarorin Boko-Haram din biyu dai basa ga maciji da juna, inda suke kaiwa juna hari akai-akai, tun bayan da wasu suka zame sukayi biyayya da kungiyar IS dake neman kafa daula a Iraki da Syria, da suka kira kansu dakarun daular musulunci a yammacin Afirka ta ISWAP.

ISWAP ta yi karfi sosai

Bayanai na cewa bangaren na ISWAP tayi karfi cikin kungiyar da ta kwashe sama da shekaru goma tana kai kazaman hare-hare a yankin arewa maso gabashin Najeriya, wanda ya kashe sama da mutane dubu 40 tare da tilastawa sama da miliyan 2 da gidajensu, kafin fadada farmaki wasu yankunan kasashen Kamaru da Chadi da kuma Nijar.

Sojoji basu tabbatar ba

Ya zuwa yanzu dai, rundunar sojin Najeriya batayi tsokaci dangane da wannan batu ba, ko da da AFP ya tuntubi kakakin rundunar Mohammed Yerima yace suna gudanar da binkice akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.