Najeriya-Boko Haram

Boko Haram na shirin kai hari Abuja da Jos- Sufeton Janar

Wasu mayakan Boko Haram.
Wasu mayakan Boko Haram. AFP

Sufeto Janar na 'yan Sandan Najeriya Usman Baba ya bayyana cewar mayakan boko haram na kitsa shirin kai hari birnin Abuja da Jos da ke Jihar Plateau, abinda ya sa kwamishinonin Yan Sandan wadannan Yankuna cikin shirin ko ta kwana.

Talla

Baba ya ce bayanan asiri da suka samu ya nuna musu cewar bangaren boko haram dake karkashin Muhammad Sani dake da cibiya a Sambisa da kuma mataimakin sa Suleiman dake Jihar Yobe ke shirya kai harin.

Bayan gargadin jami’an Yan Sandan dake wadannan yankuna wajen ganin sun zauna cikin shirin ko ta kwana, Sufeto Janar din ya kuma bukaci mazauna yankunan su dinga sanya ido kan abinda ke faruwa kusa da su wajen kai rahoto ga jami’an tsaro kan abinda basu gamsu da shi ba.

Wannan mataki na zuwa ne makwanni bayan da gwamnan jihar Niger Sani Bello ya bayyana cewar birnin Abuja na cikin hadari ganin yadda suka mamaye wani yanki na jihar sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI