Najeriya

Shugaban sojin kasan Najeriya Lafatanar Janar Ibrahim Attahiru ya rasu

Shugaban sojin kasan Najeriya Lafatanar Janar Ibrahim Attahiru ya rasu yau sakamakon hadarin jirgin sama a Jihar Kaduna 21 ga watan Mayu 2021
Shugaban sojin kasan Najeriya Lafatanar Janar Ibrahim Attahiru ya rasu yau sakamakon hadarin jirgin sama a Jihar Kaduna 21 ga watan Mayu 2021 © Nigerian Army

Ana cigaba da aikewa da sakwannin ta’aziyar babban hafsan rundunar sojin kasan Najeriya Janar Ibrahim Attahiru da ya rasu sakamakon hatsarin jiragin saman da ya rutsa da shi.

Talla

Rundunar sojin Najeriya tace Janar Attahiru ya rasu tare da jami’an sa ne a lokacin da jirgin da suke ciki ya fadi yayin ziyarar aiki a Kaduna.

Bayanai sun ce mutane 11 ke cikin jirgin yakin Najeriyar da yayi hatsarin dauke da babban hafsan sojin, wanda aka nada shi kan mukamin a ranar 26 ga watan Janairun day a gabata.

Daraktan yada labaran sojin saman Najeriya Edward Gabwet ya tabbatar da aukuwar hatsarin a kusa da tashar jiragen saman Kaduna, amma ba tare da karin bayani kan mutanen dake cikin jirgin ba, ko da ya ke wasu majiyoyi sunce mutane 12 ke ciki.

Wani lokaci a yau Asabar ne za a yi jana'izar babban hafsan na rundunar sojin kasan Najeriya a Abuja.

Wanene Attahiru?

An haifi Laftanar Janar Ibrahim Attahiru ne a ranar 26 ga watan Janairun shekarar 2021 a Doka dake karamar hukumar Kaduna ta Arewa, kuma ya halarci Cibiyar horar da sojojin Najeriya ta NDA.

Janar Attahiru ya rike mukamai da dama bayan kammala karatun sa wadanda suka hada da aiki a karkashin Majalisar Dinkin Duniya a Saliyo da aiki a rundunar ECOMOG dake Liberia.

Ya kuma rike mukamin kwamanda a Bataliya ta 146 dake bakassi da Birget na 13 da shugaban rundunar yaki da book haram da Babban kwamandan ruduna ta 82 kafin nada shi a matsayin shugaban sojin kasa na Najeriya a wannan shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI