Najeriya

Mutane akalla 70 sun jikkata sakamakon fashewar tanka a Kano

Wani yanki na birnin Jihar Kano a Najeriya.
Wani yanki na birnin Jihar Kano a Najeriya. © REUTERS/LUC GNAGO

Akalla Mutane kusan 70 aka bayyana sun samu raunuka daban daban sakamakon gobarar da wata tankar daukar mai tayi a birnin Kano dake Najeriya a yammacin jiya.

Talla

Rahotanni sun ce tankin ta kama wuta ne lokacin da take sauke mai a wani gidan mai dake Unguwar Sharada a cikin birnin.

Wasu masu sana'o'i a jihar Kano dake arewacin Najeriya.
Wasu masu sana'o'i a jihar Kano dake arewacin Najeriya. © Luc Gnago/Reuters

Bayanan da muka samu sun ce daga cikin wadanda suka samu raunuka harda jami’an agajin gaggawa na jihar Kano dake kokarin kashe wutar.

Kakakin hukumar kashe gobarar Jihar Kano Saminu Yusuf Abdullahi yace ma’aikatan su guda 8 na daga cikin mutane 64 da suka samu raunuka a hadarin.Ya zuwa yanzu dai babu labarin rasa rai a gobarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI