Najeriya-Tsaro

Najeriya: An tsige hakimin Kankara saboda laifin taimaka wa 'yan bindiga

Makarantar sakandaren garin Kankara dake jihar Katsina a arewacin Najeriya, inda 'yan bindiga suka sace dalibai fiye da 300, kafin daga bisani su sako su bayan kwanaki 6.
Makarantar sakandaren garin Kankara dake jihar Katsina a arewacin Najeriya, inda 'yan bindiga suka sace dalibai fiye da 300, kafin daga bisani su sako su bayan kwanaki 6. AP - Abdullatif Yusuf

A Najeriya gwamnatin  jihar Katsina ta sauke hakimin Kankara,  Alhaji Yusuf Lawal saboda samun sa da laifin taimaka wa ‘yan bindiga.

Talla

A ranar 12 ga watan Disamban shekarar 2020 ne wani kwamandan daji, Auwalun Daudawa, wanda ya gamu da ajalinsa kwanan nan ya sace dalibai sama da 300 a garin Kankara, satar dalibai na farko da wata kungiyar masu aikata laifi ta taba yi, bayan Boko Haram.

Sakataren karamar hukumar, Alhaji Bello Mamman-Ifo, ne ya bada sanarwar, ta bakin jami’ain yada labaran masarautar, Alhaji Ibrahim Bindawa, a Katsina.

Ya ce binciken da suka gudanar a kan zargin da ake wa hakimin kan taimaka wa ‘yan ta’adda ya nuna cewa lallai ya aikata laifin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI