Najeriya - Ta'addanci

‘Yadda rashin tsaro ya yi wa tattalin arzikin arewacin Najeriya illa’

'Monday Market' daya daga cikin kasuwanni mafi girma da kuma bunkasar hada-hada a birnin Maiduguri dake jihar Borno, wadda ta fuskanci jerin hare-haren 'yan kunar bakin wake na kungiyar Boko Haram, sai dai barazanar tsaron bai hana ta cigaba da wanzuwa ba. 26/7/2019.
'Monday Market' daya daga cikin kasuwanni mafi girma da kuma bunkasar hada-hada a birnin Maiduguri dake jihar Borno, wadda ta fuskanci jerin hare-haren 'yan kunar bakin wake na kungiyar Boko Haram, sai dai barazanar tsaron bai hana ta cigaba da wanzuwa ba. 26/7/2019. RFI/Fati Abubakar

Kafin shekara ta 2007, Yankin Arewacin Najeriya ke sahun gaba wajen ayyukan samar da abincin da ya shafi noma da kiwo ga daukacin Najeriya da  kasashen dake makotaka da ita, tare da gudanar da harkokin kasuwanci.

Talla

Sai dai rikicin Boko Haram da a yanzu haka ya kai shekaru 14 ba tare da gushewa ba, yayi kuma matukar illa ga Jihohin Borno da Yobe da Adamawa wadanda ke sahun gaba wajen harkar noma da kiwo ganin yadda yayi sanadiyar mutuwar mutane kusan dubu 40,000 da kuma raba sama da wasu miliyan biyu da rabi daga matsugunan su a yankin.

Sansanin Muna dake garin Maiduguri mai dauke da dubban 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu. 1/12/2016.
Sansanin Muna dake garin Maiduguri mai dauke da dubban 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu. 1/12/2016. © REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo

Wannan rikici ya kuma hana dubban mutane zuwa gonakinsu, matsalar da ta taimaka wajen rage gonakin da aka saba nomawa da kuma takaita abincin da ake samarwa ta hanyar noma da kiwo.

Harkokin kasuwanci ma basu tsira ba a wannan yanki mai dimbin jama’a, ganin yadda rayuwa ta tagayyara, zirga zirga suka takaita, mu’amala ta fuskanci koma baya, jama’a suka koma zama cikin mummunan yanayin fargaba da kuma shakku kan abinda kan iya zuwa ya komo.

Yayin da ake kokarin shawo kan wannan matsala ta Boko Haram da ta takaita a Jhihohi 3 na Arewa maso Gabashin Najeriya, da kuma wasu sassan kasashen Nijar da Kamaru da Chadi, sai kuma matsalar ‘yan bindiga barayin shanu ta bullo a Yankin Arewa Maso Yammacin Najeriya, kuma nan da nan ta yadu zuwa daukacin Jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna da kuma Niger wajen kashe makiyaya ana kwashe shanunsu.

Hoto domin misalin dake siffanta 'yan bindiga a Najeriya.
Hoto domin misalin dake siffanta 'yan bindiga a Najeriya. REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo

Ganin yadda matsalar ta fadada ta sanya akasarin makiyayan dake wadannan yankunan suka rabu da dabbobin su da suka saba rayuwa da su, yayin da wasu da dama kuma suka rasa rayukansu, ba tare da hukumomin da alhakin ya rataya kansu sun dauki matakan da suka dace ba wajen dakile wannan aika aika.

Wannan ya sa wasu da aka raba su da dabbobinsu, suma suka dauki makamai suka shiga cikin jerin masu aikata laifuffuka na fashi da makami da garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da kuma kai munanan hare hare garuruwa suna kashe mutane baji ba gani.

Yayin da ake fama da wannan matsalar, harkokin yau da kullum a wadannan yankuna sun gagara, manoma sun kasa zuwa gonakinsu, ‘yan kasuwa sun daina tafiye tafiyen da suka saba domin gudanar da harkokin kasuwancinsu, saboda yadda 'yan bindiga ke tare hanya suna farautarsu suna kuma kashe mutane da kuma garkuwa da wasu.

Rahotanni sun ce wasu yankunan har haraji suke baiwa wadannan ‘yan bindiga kafin zuwa gonakin da za su noma, haka kuma suke biyan kudi kafin girbi domin kawo abincin da suka noma zuwa gida.

Wasu makiyaya yayin kiwon dabbobinsu a wajen garin Zaria dake jihar Kaduna a Najeriya. 15/11/2016.
Wasu makiyaya yayin kiwon dabbobinsu a wajen garin Zaria dake jihar Kaduna a Najeriya. 15/11/2016. REUTERS - AKINTUNDE AKINLEYE

Sannu a hankali wannan matsala ta fadada zuwa akasarin Jihohin dake arewa maso yamma da kuma wasu jihohin dake Arewa ta Tsakiya, harma da birnin Abuja, cibiyar gwamnatin Najeriya, saboda yadda ake kai hari ana sace mutane a gidajen su ko kuma a tare su akan hanya.

Shi kuwa yankin Arewa ta Tsakiya na fama ne da rikicin manoma da makiyaya da kuma kabilanci da na addini wanda yayi masa matukar illa ganin irin asarar rayuka da kuma dukiyoyin jama’a da ake yi.

Wadannan dimbin matsaloli yanzu haka sun yiwa yankin arewacin Najeriya matukar illa wajen hana noma da kiwo a sassa daban daban da kuma hana harkokin kasuwanci saboda hatsarin dake tattare da tafiye tafiye a yankin baki daya sakamakon ayyukan ‘yan bindiga.

Bakin 'yan kasuwa na fargabar zuwa Najeriya saboda rashin tsaro

Wannan tashin hankali ya kuma hana bakin ‘yan kasuwar da suka saba zuwa daga kudancin Najeriya zuwa yankin da ma masu zuwa daga kasashen dake makotaka da Najeriya, harma da masu zuba jari dake shigowa Najeriya daga kasashen duniya.

Yau ta kai ga dubban mutanen da wadannan matsaloli suka addabi yankunansu, sun talauce saboda asarar ‘yan uwansu da dukiyoyinsu da ma gonakinsu da basa iya zuwa nomawa saboda fargabar abinda ke iya faruwa da su daga irin wadannan mahara.

Dalilin wannan matsala, tattalin arzikin yankin arewacin Najeriya na cigaba da tagayyara, rayuwar jama’a na dada shiga halin kunci da fargaba a koda yaushe, yayin da harkokin kasuwanci suka tsaya cik a yankin.

Mazauna wannan yankin sai dada talaucewa suke sakamakon wadannan matsaloli, yayin da wasu ke kaura zuwa wasu yankunan koma barin kasar baki daya domin samarwa kan su mafita daga wannan al’amari.

Wani kauye da 'yan bindiga suka tilastawa mutane masu yawan gaske tsrewa a karamar hukumar Jibiya dake jihar Katsina a Najeriya.
Wani kauye da 'yan bindiga suka tilastawa mutane masu yawan gaske tsrewa a karamar hukumar Jibiya dake jihar Katsina a Najeriya. © Daily Trust

Rahotanni sun ce yanzu haka garuruwa da kauyuka da dama dake yankunan karkara a Jihohin Arewa maso Yamma sun zama kufai sakamakon tserewar da mazauna garuruwan suka yi domin kaucewa hare haren wadannan ‘yan ta’adda da basu mayar da ran Bil Adama komai ba.

Yau gidaje da dama sun talauce saboda yadda gidaje suke karyar da kadarorinsu da suka hada da gidaje da gonaki da ababen hawa suna sayarwa domin biyan kudaden fansar kubutar da ‘yan uwansu da suka fada tarkon masu garkuwa da mutane domin ceto rayukansu. Wasu daga cikinsu ma basa kubuta ko da an biya kudin fansar sai an kasha su.

Wasu sojojin Najeriya.
Wasu sojojin Najeriya. © AFP

Gwamnatin Najeriya dai tace tana iya bakin kokarin ta wajen ganin ta shawo kan wadannan dimbin matsalolin da suka addabi Yankin da ma kasa baki daya, amma ga alama har yanzu akwai sauran aiki, domin kuwa dambu idan yayi yawa baya jin mai, a daidai lokacin da aka toshe wata kofa, sai wata ta bude dangane da dimbin matsalolin tsaron da suka addabi Yankin arewacin Najeriya da kuma kasar baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI