Abuja-Najeriya

Mutanen Neja sun toshe hanyar Abuja don bore kan satar mutane

Masu zanga-zanga sun kuma kona tayoyi akan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna
Masu zanga-zanga sun kuma kona tayoyi akan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna © The Guardian Nigeria

Yanzu haka ana gudanar da zanga-zanga a garin Gauraka da ke kan  babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna a jihar Neja da ke Najeriya, inda fusatattun mutanen yankin suka toshe tituna domin nuna bacin ransu kan tsanantar sace-sacen jama’a.

Talla

Zanga-zangar ta haddasa cinkoson ababawan hawa tun daga yankin har zuwa barikin sojoji na Zuma da kuma Madalla da wasu sassan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Rahotanni sun tabbatar cewa, masu zanga-zangar sun kona ofishin ‘yan sanda da ke yankin.

Kazalika masu boren sun cinna wa wata mota wuta da ake zargin ta kwaso masu garkuwa da jama’a a yanikin Madalla.

Garin Gauraka na cikin yankunan jihar Neja da ‘yan bindiga suka matsa musu ta hanyar kaddamar musu da hare-hare da kuma sace mutanensu domin karbar kudin fansa.

Ko a ‘yan kwanakin nan, sai da ‘yan bindigar suka dirar wa  garin kuma suka sace mutanen da kawo yanzu babu wanda ya san halin da suke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI