Najeriya-IPOB

Kungiyar IPOB ta sake kai farmaki Ofishin 'yan sanda a jihar Imo

Gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma lokacin da yake ziyarar gani da ido kan barnar da mayakan IPOB suka yi a ofishin yan sandan Oweeri 5 ga watan Afrelu 2021
Gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma lokacin da yake ziyarar gani da ido kan barnar da mayakan IPOB suka yi a ofishin yan sandan Oweeri 5 ga watan Afrelu 2021 AP - David Dosunmu

A Najeriya wasu bayanai na cewa 'yan bindigar da ake kyautata zaton ’ya'yan kungiyar IPOB ne da gwamnatin kasar ta haramta, sun sake kai hari wani ofishin 'yan Sanda da ke Orji a Jihar Imo.

Talla

Rahotannin da Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a kasar ta ruwaito sun ce da misalin karfe 12 na ranar yau ‘ya'yan kungiyar dauke da makamai suka afkawa tashar 'yan sandan, abinda ya haifar da musayar wuta tsakanin bangarorin biyu.

Wannan hari na zuwa ne bayan wani dan lokaci da wadanda ake zargin sun kai hari tashar Yan Sandan dake Iwollo Oghe a karamar hukumar Ezeagu dake Jihar Enugu.

Bayanan dake fitiwa daga yankin sun ce an hallaka wasu jami’an Yan Sanda lokacin harin, yayin da aka bankawa ofishin nasu da motocin dake wurin wuta.

Kakakin rundunar Yan Sandan Jihar Daniel Ndukwe ya tabbatar da kai harin, amma bai yi karin haske kan irin ta‘adin da akayi ba.

Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma ya sha alwashin amfani da jami’an tsaro wajen shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi jihar sa, cikin su harda irin wadannan hare hare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI