Shekaru 22 da dawowar dimokiradiya Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AP - Bayo Omoboriowo

Yau Najeriya ke bikin cika shekaru 22 da sake dawowar dimokiradiya a cikin kasar bayan juyin mulkin da soji suka yi a shekarar 1984 wanda ya katse Jamhuriya ta biyu a karkashin mulkin shugaban kasa Alh Shehu Usman Aliyu Shagari.

Talla

Olusegun Obasanjo ne shugaba na farko da ya karbi ragamar tafiyar da kasar a karkashin sabuwar Jamhuriya ta 4 a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 1999, inda ya kwashe shekaru 8 yana mulkin kasar bayan ya samu nasarar zabe zagaye na biyu.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan dake zama babban Jakadan kungiyar ECOWAS a kokarin sasanta rikicin siyasar kasar Mali.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan dake zama babban Jakadan kungiyar ECOWAS a kokarin sasanta rikicin siyasar kasar Mali. © Presidency of Nigeria

Bayan kammala mulkin shugaba Obasanjo, Yan Najeriya sun zabi Malam Umaru Musa Yar’adua a matsayin shugaban kasa a shekarar 2007 amma bayan kusan shekaru 2 sai ya rasu sakamakon rashin lafiya, abinda ya baiwa mataimakin sa Goodluck Jonathan damar karbar ragamar mulki da kuma sake zaben sa a shekarar 2011.

A shekarar 2015 an zabi Janar Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa, kuma ya sake samun nasara a zaben shekarar 2019.

Yaya kuke kallon wannan tafiya na mulkin dimokiradiya a Najeriya?

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI