Najeriya - Muhammadu Buhari

'Yan Najeriya za su yi kewar Buhari bayan saukarsa - Adesina

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari © Twitter / @MBuhari

Yau Asabar 29 ga watan Mayu, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke cika shekaru 6 cif da darewa bisa kujerar shugabancin kasar.

Talla

Dangane da cikar shekarun 6 ne kuma a jiya Juma’a mashawarcin shugaban Najeriya kan yada labarai Femi Adesina ya ce ‘yan Najeriya za su yabawa gwamnatin Buhari a karshen mulkinsa bayan bayyanar namijin kokarin da yayi wajen jagorantar kasar.

A cewar Adesina sannu a hankali nasarorin da gwamnati mai ci ke samu za su rika bayyana wadanda za su gadar musu da jinjinar ban girma.

Sai dai babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriyar, ta kulabalanci shugaban kasar da yayi amfani da jawabin da zai gabatar a yau din kan cikarsa shekaru 6 bisa Mulki, wajen neman afuwar ‘yan Najeriya da kuma amincewa ga gazawar gwamnatinsa kan shugabanci nigari.

Cikin sanarwar da ya fitar kakakin jam’iyyar ta PDP Kola Ologbondiyan ya bukaci shugaba Buhari da jam’iyyar sa ta APC da su kawo karshen gabatar da jawabai masu cike da alkawuran da basa iya cikawa ‘yan Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI