Najeriya - Siyasa

An kaiwa ofisoshinmu 41 farmaki cikin shekaru 2 - INEC

Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC, farfesa Mahmoud Yakubu.
Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC, farfesa Mahmoud Yakubu. © The Guardian Nigeria

Hukumar Zabe a Najeriya na cigaba da bayyana fargaba kan makomar zaben shekarar 2023 ganin yadda ake cigaba da kaiwa ofisoshin ta hare hare ana kona kayayyakin dake ciki wadanda ke barazana ga zaben mai zuwa.

Talla

Shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakubu ya ce a cikin shekaru 2 da suka gabata an kaiwa ofisoshin ta 41 hari kuma anyi nasarar lalata kayan aikin dake ciki sakamakon tashin hankalin dake da nasaba da zabe da rikicin da bashi da nasaba da zaben da kuma ayyukan Yan banga da Yan bindiga a sassan kasar.

Jaridar Premium Times tace ta samu cikakken bayanai daga Hukumar wanda ya tabbatar da wadannan jerin hare hare da kuma garuruwan da aka kai su tsakanin watan Fabarairun shekarar 2019 zuwa Mayun wannan shekara.

Jaridar ta ce bayanan sun nuna cewar Jihar Imo ke sahun gaba wajen yawan irin wadannan hare hare daga cikin Jihohi 14 da aka samu matsalar.

Hukumar zaben tace lokacin da akayi zanga zangar adawa da cin zarafin Yan Sanda ta ENDSARS bara an kaiwa ofisoshin ta 18 hari a garuruwa daban daban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI