Najeriya - Ta'addanci

'Yan bindiga sun kashe tsohon mashawarcin Jonathan kan siyasa

Tsohon mai baiwa shugaba Goodluck Jonathan shawara kan harkokin siyasa Barista Ahmed Gulak.
Tsohon mai baiwa shugaba Goodluck Jonathan shawara kan harkokin siyasa Barista Ahmed Gulak. © TheCable

Wasu ‘yan bindiga a Jihar Imo dake Najeriya sun harbe tsohon mai baiwa shugaba Goodluck Jonathan shawara kan harkokin siyasa Barr Ahmed Ali Gulak lokacin da yake kan hanyar sa zuwa Abuja.

Talla

Wani abokin sa Dakta Umar Ardo ya tabbatar da aukuwar lamarin a sakon da ya rubuta a Facebook kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito, wanda ke tabbatar da kashe Gulak.

Dakta Ardo ya bayyana cewar a daren jiya ne Yan bindigar suka hallaka Barr Ahmed Gulak sakamakon harbe shi da suka yi.

Gulak ya taba zama shugaban Majalisar Dokokin Jihar Adamawa da kuma mai baiwa shugaba Goodluck Jonathan shawara kan harkokin siyasa lokacin da ya jagoranci Najeriya.

Jihar Imo na cigaba da fuskantar hare haren Yan bindiga da ake zargin yayan haramcaciyar kungiyar IPOB dake fafutukar kafa kasar Biafra ne.

Hare haren wadannan 'yan bindiga a Jihohin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu yayi sanadiyar kashe jami’an 'yan Sanda 127 a cikin watanni 4 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI