Birtaniya za ta taimakawa Najeriya magance matsalar tsaro a Arewa
Wallafawa ranar:
Birtaniya ta bayyana damuwa kan matsalolin tsaron da suka addabi Najeriya musamman yankin arewa maso yamma da ake cigaba da samun salwantar rayuka. Wata tawagar jami’an gwamnatin kasar da ta ziyarci da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal a birnin Sokoto ta bayyana haka. Zainab Ibrahim na dauke da rahoto akai.
Yayin ganawar da tawagar ta yi da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, shugaban tawagar gwamnatin Birtaniya Samuel Waldock ya ce gwamnatin kasar su ta damu da halin da ake ciki a Yankin Arewa Maso Yammacin Najeriya, inda yake cewa.
''Mu a matsayin na Birtaniya, muna nuna alhinin mu ga Jihar Sokoto da Jihohin dake Arewa ta Yamma kan yadda suke tinkarar wanann kalubale. Mun fahimci cewar irin illar da matsalar ta yiwa rayuka na da yawa. Mun zo nan ne domin mu bayyana goyan bayan mu ga Jihar da kuma sauran jihohin arewa maso yamma dangane da wanann batu mai muhimmanci dake da kima sosai a kasa''.
Da ya ke mayar da martani, Gwamna Aminu Tambuwal ya ce a manyan kasashen duniya, Birtaniya ce ta fi dacewa ta taimakawa Najeriya.
''Lura da tarihin mu da kuma karfin soji da tsaron da kuke da shi, babu wata kasaR da tafi dacewa da ta jagoranci tinkarar wannan kalubale a tsakanin manyan kasashen duniya da ya wuce Birtaniya wajen taimakawa kokarin Najeriya wdomin tabbatar da zaman lafiya, ba wai a yankin arewa maso yamma kawai ba, a fadin kasar baki daya''.
Jihar Sokoto na daga cikin Jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu