Mutane 7 aka kashe a rikicin da ya biyo bayan nada Sarkin Tangale - Rahoto

Wani jami'in dan sanda a tarayyar Najeriya.
Wani jami'in dan sanda a tarayyar Najeriya. AP - Sunday Alamba

Akalla mutane 7 aka tabbatar da mutuwar su, yayin da aka lalata kadarorin da yawan su ya kai 475 a tashin hankalin da ya gudana a Billiri dake Jihar Gomben Najeriya sakamakon kin amincewa da nadin Sarkin Tangale.

Talla

Shugaban kwamitin binciken da gwamnatin jihar Gombe ta kafa domin gano musabbbin rikicin da kuma abinda ya haddasa shi  Adamu Dishi ya bayyana haka lokacin da yake gabatar da rahoton aikin su ga Gwamnan Jihar Muhammad Inuwa Yahya.

Dishi yace daga cikin kadarorin da aka kona ko aka lalata akwai gidajen jama'a 41 da wuraren kasuwanci 401 da kuma wuraren ibada 33.

Yayin karbar rahotan kwamitin, Gwamna Muhammad Inuwa Yahya wanda ya bayyana bakin cikin sa dangane da lamarin ya sha alwashin aiwatar da shawarwarin da kwamitin ya gabatar bayan daukar lokaci yana bin diddigin abinda ya faru.

Gwamnan Yahya bukaci mazauna Billiri da sauran sassan Jihar Gombe da su rungumi hanyar zaman lafiya a tsakanin su ba tare da la’akari da banbancin addini ko kabila ba saboda sanin jihar a matsayin wadda tafi zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.