Najeriya-Biafra

Najeriya na zargin Twitter da taimaka wa 'yan Biafra

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. © Nigeria Presidency

Gwamnatin tarayyar Najeriya na zargin kamfanin Twitter da taka rawa a fafutukar mayakan Biafra masu neman ballewa a yankin kudu maso gabashin kasar.

Talla

Wannan na zuwa ne bayan kamfanin na Twitter ya goge kalaman shugaba Muhammadu Buhari da aka watsa a shafinsa, inda ya ce, za su dauki mataki kan wadanda ke kokarin wargaza Najeriya.

A shafin nasa, shugaba Buhari ya ce, 

Akasarin wadanda ke wuce gona da iri a yau, matasa ne da ba su da masaniya kan asarar rayukan da aka samu a lokacin yakin basasar Najeriya.  Mu da muka kwashe watanni 30  a fagen-daga, za mu fahimtar da su ta hanyar da ta dace .

Sai dai kamfanin na Twitter ya share wadannan  kalamai na Buhari, yana mai cewa, hakan ya saba wa ka’idojinsa, sannan kuma ya samu korafe-korafe daga jama’a.

A yayin mayar da martani, Ministan Yada Labarai na Najeriya Lai Mohamed ya ce, cikin ruwan sanyi, shafin na Twiiter ya kawar da kai daga kalaman Nnamdi Kanu, shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB da mukarrabansa.

Minisatan ya ce, Twitter ya kawar da kai daga kalaman Kanu da ke tunzira kashe-kashen  jami’an ‘yan sanda, sannan kuma ya nuna son-kai a yayin zanga-zangar ENDSARS, lokacin da matasa suka lalata tare da sace kadarorin gwamnati da sunan ‘yanci.

Ministan ya ce, ya yi mamakin yadda kamfanin ke kallon kalaman Buhari a matsayin masu tayar da hankula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI