Najeriya - Coronavirus

Najeriya ta damu bayan da India ta dakatar da allurar rigakafin korona kasar

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da wasu mukarrabansa yayin ganawa a fadar gwamnati. Rarar 2 ga watan Yuni shekarar 2021
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da wasu mukarrabansa yayin ganawa a fadar gwamnati. Rarar 2 ga watan Yuni shekarar 2021 © Bashir Ahmad

Mahukuntan Najeriya sun nuna fargabarsu sakamakon dakatar da shigo da Allurar rigakafin COVID 19 da kasar India ta yi, sakamakon yadda cutar ta yi mata kamarin, lamarin da mahukunta ke cewa ya tilasta musu neman samar da Allurar a cikin gida domin kaucewa fadawa matsala. Inda suka ce izuwa yau din nan mutane miliyan 1 da dubu 961 suka karbi Allurar kashin Farko. Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron rahoton Mohammed Kabir Yusuf daga Abuja