Najeriya - Ta'addanci

"Sojojin kasa kadai ba za su iya magance matsalolin tsaron Najeriya ba"

Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya Manjo Janar Farouk Yahaya.
Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya Manjo Janar Farouk Yahaya. © World News

Babban hafsan sojin kasa na Najeriya Manjo Janar Farouk Yahaya ya ce dakarunsa kadai ba za su iya kawo karshen matsalolin tsaron da suka addabi sassan Najeriya ba.

Talla

A cewar babban hafsan sojin kasan dole ne a samu hadin gwiwa tsakanin dukkanin rundunonin tsaron Najeriya kafin samun nasarar murkushe ‘yan ta’addar da suke neman yiwa Najeriya kofar rago.

Manjo Janar Yahaya Farouk ya bayyana haka ne a birnin Abuja, lokacin da ya ziyarci takwaransa, babban hafsan rundunar sojin saman Najeriya Air Marshal Oladayo Amao.

Shugaban dakarun na kasa ya bayyana gudunmawar sojojin sama a matsayin ginshiki mai karfi wajen samun nasara kan dukkanin farmakin da takwarorinsu na kasa za su kaddamar, kamar yadda ya gani a ayyukan filin dagar da ya jagoranta a lokutan baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.