Cutar korona ta kashe karin mutane 18 a Najeriya

Wani jami'in kula da lafiya na karbar allurar rigakafi a Dakar dake kasar Senegal ranar 24 ga watan Fabararirun shekarar 2021
Wani jami'in kula da lafiya na karbar allurar rigakafi a Dakar dake kasar Senegal ranar 24 ga watan Fabararirun shekarar 2021 REUTERS - ZOHRA BENSEMRA

Hukumar yaki da cututtuka a Najeriya ta sanar da cewar mutane 18 suka mutu a ranar alhamis sakamakon kamuwa da cutar korona a daidai lokacin da ake samun karuwar masu harbuwa da ita a fadin kasar.

Talla

Wannan sabon adadi ya nuna karuwar yawan mutanen da suka mutu tun bayan barkewar cutar a Najeriya bara zuwa 2,117 daga cikin mutane 166,682 da aka tabbatar sun harbu da ita.

Alkaluman hukumar sun nuna cewar a jihar Lagos kawai mutane 105 aka gano sun harbu da cutar jiya alhamis, kwana guda bayan an gano cewar babu wanda ya rasa ran sa sakamakon cutar a Najeriya a ranar laraba.

Har yanzu jihar Lagos ke sahun gaba wajen samun yawan wadanda suka harbu da cutar da suka kai 59,057 wanda ya zarce kashi daya bisa uku na yawan mutanen Najeriya a cutar ta kama, kuma daga cikin su 439 sun mutu, yayin da kusan 57,000 suka warke.

Hukumar tace tayi nasarar yiwa mutane miliyan 2 da dubu 113 da 061 gwajin cutar daga cikin mutanen kasar sama da miliyan 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.