Kotu ta haramtawa Hukumar dake kula da majalisa sanya albashin Yan Majalisu

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan Twitter/Nigerian Senate

Wata Babbar Kotu a birnin Lagos dake Najeriya ta yanke hukuncin cewar Hukumar dake kula da ma’aikatan Majalisar dokokin kasar bata da hurumin sanya albashin Yan Majalisun Dattawa 109 da na wakilai 360 domin hurumi ne na Hukumar tara kudaden haraji ta kasa.

Talla

Yayin yanke hukunci kan wata karar da kungiyar SERAP dake fafutukar ganin an aiwatar da gaskiya da wasu kungiyoyi da kuma mutane sama da 1,500 suka sanya hannu akai, alkalin kotun Chuka Austine Obiozor yace Hukumar kula da majalisar bata da hurimi dangane da sanya albashi da alawus-alawus da ake biyan Yan majalisun tarayyar.

Alkalin kotun yace Hukumar tara kudaden harajin ne alhaki ya rata akan ta kuma ita kadai ke da hurumin sanya albashi da alawus na Yan Majalisun da masu rike da mukaman siyasa.

Wannan hukunci ba karamar nasara bace ga kungiyoyi da kuma daidaikun Yan Najeriya dake korafi kan yawan kudin da ake biyan Yan Majalisun a matsayin albashi da alawus kowanne wata lura da halin kuncin da jama’ar kasar ke fama da ciki.

Mataimakin Daraktan kungiyar SERAP Kolawole Oluwadare ya yaba da hukuncin wanda yace zai taimaka wajen rage makudan kudaden da ake kashewa Yan Majalisun

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.