Yan bindigar da suka sace daliban Tegina sun kara yawan kudin fansa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya baiwa jami'an tsaro umurnin kubutar da daliban
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya baiwa jami'an tsaro umurnin kubutar da daliban Ludovic MARIN POOL/AFP/File

Yan bindigar da suka sace daliban makarantar Islamiya a Tegina dake Jihar Naijar Najeriya sun kara yawan kudin fansar da suke bukata daga naira miliyan 130 zuwa naira miliyan 200.

Talla

Shugaban makarantar Islamiyar Abubakar Alhassan ya bayyana kara kudin fansar da 'yan bindigar suka yi daren jiya alhamis yayin tattaunawa da RFI Hausa kan halin da yaran suke ciki da kuma kokarin kubutar da su.

Malamin yace ya zuwa lokacin sunyi nasarar tara kudin taimako da ya kai naira dubu 350 daga hannun jama’a amma kuma babu wani abinda ya fito daga hannun gwamnatin jiha ko ta kasa baki daya.

Alhassan yace a lokacin da yayi magana da daya daga cikin malaman makarantar dake tare da daliban da aka sace an shaida masa cewar an tube yaran a wannan yanayi na damina da ake tafka ruwan sama.

Malamin wanda ‘yayan sa guda 2 ke cikin daliban da aka sace ya bayyana matukar damuwa kan halin da daliban nasa suka samu kan su da kuma abinda zai zama makomar su a hannun Yan bindigar da suka katse magana da shi bayan cikar wa’adin jiya da suka basu domin biyan kudin fansar.

Rahotanni daga garin Tegina sun tabbatar da mutuwar biyu daga cikin iyaye mata na wadannan dalibai sakamakon samun labarin sace ‘yayan su da akayi a wannan makarantar Islamiya.

Jihar Naija dake Najeriya na daya daga cikin jihohin arewacin Najeriya da sata da garkuwa da mutane ke kara samun gurbin zama sakamakon tabarbarewar tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.