Gwamnatin Borno ta haramta sayar da gawayi da itace a Maiduguri

Gwamnan jihar Barno dake Najeriya Babagana Umara Zulum
Gwamnan jihar Barno dake Najeriya Babagana Umara Zulum RFI hausa/Abba

Gwamnatin Jihar Barno dake Najeriya ta haramta sayar da gawayi da kuma itace a titunan birnin Maiduguri a wani shirin rage yawan itatuwan da ake sarewa domin yin girki a yunkurin ta na kare muhalli.

Talla

Gwamnatin ta kuma baiwa masu sayar da itace umurnin sa’oi 48 na komawa wata kasuwa ta musamman dake kan hanyar Damboa domin tantance masu sare itatuwan suna kaiwa kasuwa.

Kwamishinan shari’ar Jihar Kaka-Shehu Lawal ya bayyana haramcin wajen bikin dasa itatuwa da aka gudanar yau wanda yayi daidai da ranar bikin kare muhalli ta duniya.

Lawal yace gwamnatin Barno ta jagoranci shuka itatuwan neem sama da miliyan guda a fadin jihar, yayin da ya bayyana aniyar su ta goyawa kungiyoyi masu zaman kan su da hukumomi baya domin shuka itatuwa a jihar.

Mataimakin Gwamnan Jihar Umar Usman Kadafur da ya halarci bikin yace an shuka nau’oin itatuwa daban daban har 5,000 a jihar, yayin da za’a shuka wasu Karin 500,000 a yankunan ta baki daya.

Jihar Barno na daya daga cikin jihohin dake fama da matsalar kwararowar hamada, yayin da jama’ar ta ke cikin wadanda ke sare itatuwa domin yin girki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.