Najeriya-Twitter

Gwamnatin Najeriya za ta hukunta duk wanda ya karya dokar dakile Twitter

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Twitter@BashirAhmaad

Gwamnatin Najerya ta sha alwashin hukunta duk wanda aka kama yana saba wa dokar haramta amfani da dandalin sadarwar Twitter.

Talla

Tuni ministan  shari’a na kasar Abubakar Malami  ya yi umurnin da a gaggauta gurfanar da wadanda aka kama su na saba wa wannan haramci.

A ranar Juma’a ne ministan yada labaran kasar Lai Mohammed ya sanar da matakin gwamnati na dakatar da ayyukan Twittar a Najeriya.

Wannan na zuwa ne bayan da dandalin ya sauke wani bayani da shugaban kasar ya wallafa a shafinsa na Twitter a game da yakin basasa, yana mai cewa ya saba wa ka’idansa.

Amma duk da wannan haramcin ‘yan Najeriya da dama sun koma amfani da wata manhaja  mai zaman kanta  ta VPN da ke ba su damar shiga Twitter duk da dakile shi da kamfanonin wayar sadarwar kasar suka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.