Najeriya - 'Yan bindiga

'Yan bindiga sun sace wani dan kasuwa a Kano

Wani dan bindiga dauke da makami a Najeriya
Wani dan bindiga dauke da makami a Najeriya © Social News XYZ

Rundunar ‘yan sandar jihar Kano dake Najeriya ta tabbatar da sace wani dan kasuwa a garin Kore na karamar hukumar Dambatta da wasu‘ yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka yi.

Talla

Rahotanni suka ce  'yan bindigar sun mamaye garin ne cikin daren Alhamis, inda suka yi  ta harbi babu kakkautawa kafin suyi awon gaba da Emmanuel Eze lokacin da yake shagon.

Kakakin rundunar 'yan sandan Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce tuni kwamishinan' yan sanda na jihar, Sama'illa Shua'ibu Dikko, ya aike da wata tawagar jami'an 'yan sanda don tabbatar da ceto wanda lamarin ya rutsa da shi cikin gaggawa, da kuma kama masu satar mutane.

Ya zuwa yanzu dai masu garkuwan ba su tuntubi dangi don neman kudin fansa ba, amma lamarin ya jefa mutanen yankin cikin fargaba.

Wannan na zuwa ne kwana daya kacal bayan da Gwamnan jihar  Abdullahi Umar Ganduje ya yi gargadi game da shigowar 'yan bindiga cikin dazukan Kano.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI