Najeriya-Twitter

Najeriya ta gindayawa twitter sharudda - Minista

Shugaban Najeria Muhammadu Buhari
Shugaban Najeria Muhammadu Buhari Ludovic MARIN POOL/AFP/File

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewar kamfanin twitter ya tintibe ta domin warware matsalar da aka samu wadda tayi sanadiyar dakatar da ayyukan sa a cikin kasar, yayin da aka gindaya masa sharidodin da ake bukatar ya cimma

Talla

Ministan yada labaran kasar Alhaji Lai Mohammed ya bayyana tintibar da kamfanin ya yiwa gwamnatin bayan wani taron majalisar zartarwar kasar wadda ake gudanarwa mako-mako.

Mohammed ya bayyana cewar kamfanin twitter ya baiwa wadanda ke yiwa cigaban dorewar Najeriya barazana da kuma baiwa masu zanga zangar adawa da cin zarafin Yan Sanda ta ENDSARS kudade da kuma baiwa shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra ta IPOB Nnamdi Kanu damar amfani da dandalin sa wajen kiran magoya bayan sa su kai hari domin kashe jami’an Yan Sanda.

Ministan yace kamfanin twitter yayi watsi da bukatar gwamnati na goge sakwannin Nnamdu Kanu wadanda na tashin hankali ne duk da bukatar haka da aka gabatar masa.

Mohammed ya bayyana wasu sharidodi da gwamnatin ta gindayawa kamfanin twitter domin cire haramci da aka dora masa wadanda suka hada da tabbatar da samun shaidar rajista a Najeriya a matsayin kamfanin kasuwanci.

Ministan yace bayan twitter suma kamfanonin Facebook da Istagram an bukace su da su gaggauta yin rajista a cikin kasar.

Mohammed yayi watsi da masu zargin cewar an take hakkin Bil Adama wajen hana su bfadin albarkacin bakin su wajen dakatar da aikin kamfanin twitter a Najeriya, yayin da yace kamfanin ya tafka asara sosai sakamakon wannan matakin da gwamnati ta dauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.