Najeriya-Fasaha

Najeriya ta kera wayar salula ta farko a cikin gida

Shugaba Muhammadu Buhari da Ministan masana'antu Otunba Niyi Adebayo lokacin gabatar da wayar salular da akakera a Najeriya
Shugaba Muhammadu Buhari da Ministan masana'antu Otunba Niyi Adebayo lokacin gabatar da wayar salular da akakera a Najeriya © Femi Adeshina

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yau ya karbi wayar salula ta farko da aka kera a cikin kasar a karkashin jagorancin Hukumar horas da ma’aikata ta ITF.

Talla

Ministan masana’antun kasar Otunba Niyi Adebayo ya gabatarwa shugaba Muhammadu Buhari da wannan sabuwar wayar salular da aka samar wanda ke zama gagarumar cigaba daga bangaren sadarwar da aka samu a cikin gida.

Adebayo yace wani sashe dake kula da kayan lantarki na Cibiyar horar da ma’aikatar ITF ya samar da wayar ta hanyar amfani da sinadaran da aka samu a cikin Najeriya.

Ministan wanda ya bayyana farin cikin sa da wannan cigaba da aka samu ya mikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari daya daga cikin sabbin wayoyin da aka kera.

Akalla Yan Najeriya sama da miliyan 120 ke amfani da wayoyin salula a cikin kasar kuma da dama daga cikin su na amfani da waya sama da guda a lokaci daya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana matukar farin cikin sa da samar da wayar inda ya jaddada aniyar gwamnatin sa na cigaba da baiwa matasa da hukumomi goyan bayan da suke bukata domin samar da cigaba a cikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.