NAJERIYA-TATTALIN ARZIKI

Buhari ya kaddamar sufurin jiragen kasa na zamani a Lagos

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana kaddamar da shirin sufurin jiragen kasa na zamani a Lagos
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana kaddamar da shirin sufurin jiragen kasa na zamani a Lagos © Buhari Sallau

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yau ya kaddamar da aikin sufurin jiragen kasa na zamani tsakanin Birnin Lagos zuwa Ibadan daga tashar da aka yiwa suna Mobolaji Johnson dake Ebute Metta wanda ya bayyana shi a matsayin gagarumin aikin sufurin da gwamnatin sa ta saka a gaba.

Talla

Yayin kaddamar da aikin Buhari yace gwamnatin sa zata cigaba da baiwa bangaren sufurin jiragen kasa muhimmanci a matsayin kashin bayan bunkasa bangaren masana’antu da kuma tattalin arzikin kasa wanda zai taimakawa yankin Lagos da Ibadan.

Shugaban kasar yace wannan aiki zai bada damar sufurin mutane da hajjoji cikin sauki daga tashar jiragen ruwan Apapa zuwa tashar Ibadan kafin rarraba su ga sassan Najeriya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana amsa gaisuwa daga jama'a
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana amsa gaisuwa daga jama'a © Buhari Sallau

Buhari ya sake jaddada aniyar gwamnatin sa cigaba da bunkasa ayyukan sufurin jiragen kasar ta hanyar kammala aikin hanyar Lagos zuwa Kano, yayin da za’a dora daga Kano zuwa Maradi dake Jamhuriyar Nijar domin amfana da jigilar hajjojin da kasar ke shiga da su ta ruwa.

Shugaban yace kammala wannan aikin zai baiwa Yan kasuwar Jamhuriyar Nijar damar cin moriyar shirin wajen shiga da fitar da kayayyakin su zuwa kasuwannin duniya da kuma samarwa jama’a ayyukan yi.

Wasu daga cikin jiragen da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar a birnin Lagos
Wasu daga cikin jiragen da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar a birnin Lagos © Buhari Sallau

Buhari ya bayyana farin cikin sa da umurnin da ya baiwa ma’aikatar sufurin kasar wajen kammala tattaunawa da hukumomin kudaden da zasu dauki nauyin aikin tare da gwamnatin tarayya na kammala gina hanyar jirgin tsakanin Ibadan zuwa Kano.

Shugaban yace aikin hanyar Ibadan zuwa Kano zai hada zuwa Tsibirin Tin Can dake Lagos da kuma hanyoyin da zasu hada Yankin Gabashin kasar da suka hada da Calabar da Onitsha da Benin da Warri da Yenagoa da Fatakwal da Aba da kuma Uyo.

Buhari ya yabawa ministan sufuri Rotimi Amaechi saboda jajircewar sa wajen ganin aikin ya tabbata.

Bayan kaddamar da aikin shugaba Buhari ya hau jirgin daga Ebute Metta zuwa tashar Apapa  tare da shugaban majalisar dokoki Femi Gbajabiamila da Gwamnan Lagos Babajide Sanwo-Olu da kuma Gwamnonin Jihohin Ekiti da Oyo da Ogun da mataimakin gwamnan Ondo da wasu ministoci dake tawagar sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI