Harin-Yan bindiga

Mutane 500 aka kashe a Jihar Kebbi - Tukura

Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari Ludovic MARIN POOL/AFP/File

Wani Dan Majalisar Tarayya daga Jihar Kebbi dake Najeriya Kabir Ibrahim Tukura ya shaidawa Majalisar wakilai cewar akalla mutane 500 Yan bindiga suka kashe a mazabar sa ta Sakaba da Danko/Wasagu yayin da akayi garkuwa da mutane 201 bayan raba mutane sama da 15,000 da muhallin su.

Talla

Yayin da yake bayanin halin da Jihar su ta samu kan ta sakamakon hare haren Yan bindigar, Tukura yace sabanin adadin mutane 88 da Yan Sanda suka gabatar a matsayin wadanda aka kashe a makon jiya a kauyukan Koro da Kimi da Gaya da Dimi da Zulu da Rafin Gora da D’lanko da Dguenge da Chonoko da Unashi a karamar hukumar Danko/Wasagu sun gano cewar adadin wadanda suka mutun ya zarce 150.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Dan Majalisar na cewa bayan hallaka mutane an kuma sace shanu kusan 5,000 da tumaki 3,000 a cikin mako guda.

Dan Majalisar yace wadannan tarin Yan bindigar dake dauke da muggan makamai na bi gari gari suna neman shanun da zasu kwashe tare da kayan abinci da kuma satar mutane.

Tukura yace Yan bindigar sun kuma kona wasu gidaje a kauyukan da suak kai hari abinda ya jefa rayuwar wadanda suka tsira daga hare haren cikin tashin hankali.

Dan majalisar yace wadannan Yan bindiga basa barin mata ko yara yayin da suke kai irin wadannan hare hare wanda ke matukar illa ga jama’a da kuma yankunan su ganin yadda suke kasha su suke kuma yi musu fyade.

Tukura yace lura da irin wannan kisa da kuma jikkata mutane da Yan bindigar suka yi, ta tabbata cewar gwamnatin tarayya da ta jiha basa daukar matakan da suka dace domin kare rayukan jama’a, ganin yadda Yan bindigar suka mamaye wasu yankuna suna iko da su wajen yin abinda suka ga dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI