Najeriya-Tsaro

Za mu dauki matakin ba sani ba sabo kan masu barazana ga tsaro- Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Ludovic MARIN POOL/AFP/File

Sakamakon tabarbarewar tsaro a Najeriya ta yadda wasu mutane ke daukar makamai suna afkawa jami’an tsaro da fararen hula, shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bai wa jami’an tsaro umurnin daukar matakan ba sani ba sabo ga masu yi wa jama’a barazana da makamai.Tuni wasu gwamnonin jihohi kasar suka dukufa don shirya tarurukan wayar da kan jama’arsu dangane da rawar da ya kamata su taka wajen dawo da zaman lafiya a kasar.