Najeriya - Tattalin Arziki

Kasashe 4 za su sayi wutar lantarki daga Najeriya

Turakun wutar lantarki a Najeriya.
Turakun wutar lantarki a Najeriya. © Ventures Africa

Kasashen Nijar, Togo, Benin da Burkina Faso suna duba yiwuwar hada hannu domin sayen wutar lantarki daga Najeriya.

Talla

Shugaban hukumar gudanarwa ta hadakar kamfanonin lantarki da ke yammacin Afirka, Sule Abdulaziz, ya ce kasashen sun yanke shawarar sayen wutar lantarkin ne da ba a amfani da ita a Najeriya.

Najeriya, dake fama da karancin wutar lantarki ta kowane fanni, ta dade tana sayar da wutar ne ga kasashen Jamhuriyar Benin, Togo da Niger tsawon shekaru.

Amma Abdulaziz ya ce kasar za ta ci gajiyar wannan kasuwancin ta fuskar samun kudaden shiga da kuma samar da ayyukan yi.

Shugaban wanda ya bayyana hakan a taron hukumar gudanarwa ta hadakar kamfanonin lantarki dake yammacin Afirka, ya ce ana sa ran kasashen hudu za su sayi lantarkin ne kan wani sabon tsarin da aka warewa dala miliyan 570 da ake kan ginawa yanzu.

Aikin na ‘North Core’, wanda Bankin Duniya, da hukumar raya kasashe ta Faransa, da Bankin bunkasa tattalin arzikin kasashe na Afirka suka bayar da tallafin ginawa, ana sa ran kammala shi a cikin shekaru biyu masu zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.